Daga Fura Mohammed

An ayyana Ministan muhalli da albarkatun kasa na Azabaijan Mukhtar Babayev, a matsayin wanda zai shugabanci taron sauyin yanayi UNFCCC na bana COP29.

Babayev wanda ya taba shugabantar kamfanin mai na kasar Azerbaijan, SOCAR, kafin nada shi mukamin minista a shekarar 2018.

Zai kasance mutum na biyu da zai jagoranci taron na COP, wanda ya taba jagorancin matatan man fetur na baya bayan ,Sbayan Sultan Al-jaber da ya jagoranci taron na baya bayan nan daya gabata a Hadaddiyar Daular Larabawa ,wanda shine shugaban kamfanin mai na kasar ADNOC ya kuma jagoranci taron na bara.

Masu kula da lamurran da suka shafi muhalli na ganin zaɓin na Sultan al-Jaber a matsayin abin da zai dakushe muhimmancin taron duba da cewar shi ke rike da shugabancin na kamfanin man fetur na UAE.

Duk da haka, a ƙarshe ya masu nasaran samar da yarjejeniyar duniya a taron da zai kawo sauyi game da yadda ake tafi da burbushin mai, hakan ya kuma sanya wasu daga cikin masu shakku a baya zama magoya baya.

Shugabancin Baku a taron na COP na gaba a cimma shine sakamakon “tattaunawar na musamman kamar yadda jaridar “The Guardian” ta ruwaito.

Matakin dai ya janyo suka daga wasu masu rajin kare muhalli, wadanda ke nuna damuwa kan yadda za a bai wa wata kasa mai dogaro da man fetur da iskar gas damar shugabancin taron na kare dumaman yanayi.

Yayinda “Duniya za ta buƙaci ƙarin matakai don kawar da burbushin mai a COP29 ,dole ne Azerbaijan ta saurari masu sukanta , a matsayinta na mai samar da man fetur, Azerbaijan ” in ji wani mai ba da shawara.kan harkokin dumamar yanayi

Written by:

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Lets Chat
1
Need Help?
Help Center
Hello, welcome to SobiFm.How can we be of Help?