Daga Furera Mohammed

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1.3 a kasafin kudin ta na shekarar 2024 domin gudanar da ayyukan yaki da zaizayar kasa a manyan yankuna bakwai dake fadin jihar.

Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa, Hon. Mahmud Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin daya yake jawabi game da kasafin kudin ma’aikatar na muhalli a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Zamfara.

Gwamna Dauda Lawal a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba, 2023 ya gabatar da kudirin kasafin kudin jihar na Naira biliyan 423.5 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024 ga majalisar domin neman amincewar su.

Muhammad ya ce gwamnatin jihar ta ware kimanin naira biliyan 20 a cikin kididdigar shekarar 2024 don samar da ingantaccen tsarin kare muhalli, tsaftar muhalli, ayyukan sare itatuwa da sauransu.

Ya ce gwamnati za ta kuma sayo murhun wuta na zamani 12,000 domin rabawa magidanta marasa galihu a karkashin shirin hassasa kare dumamar yanayi na Gwamnatin Dauda Lawal.

A cewarsa, “aikin zai kuma rage fitar da iskar Carbon mara inganci da jawo hankalin jihar wajen dakile sare itatuwa da gurbata muhalli.

“Wannan zai zama babban tasiri ga jihar saboda zai rage matsalolin kiwon lafiya daban-daban dake afkuwa dalilin amfani da itacen wuta wanda ke haifar da hayaki da ke haifar da haɗari ga lafiyar ɗan adam,” in ji shi.

Ya kuma ce za a kara sayo motoci da na’urorin tsaftace muhalli domin tabbatar da tsaftar muhalli.

Written by:

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Lets Chat
1
Need Help?
Help Center
Hello, welcome to SobiFm.How can we be of Help?