Daga Fura Mohammed

Gwamnatin tarayya ta sake jaddada kudirinta na gyara kasa data gurbatace a kasar nan domin dorewar gyaran kasa da muhalli .

Ministan Muhalli Malam Balarabe Lawal ne ya ba da wannan tabbacin a taron masu ruwa da tsaki na kwamitin gudanarwa kan inganta yanayi tarayya da na Jihohi mai taken( Agro-Climate Resilience in Semi-Arid Landscapes) (ACReSAL) da aka gudanar a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023, a Abuja.

Da ya kunshe jami,ai daga Ma’aikatar Muhalli, Noma , Abinci ,Ruwa , Tsaftar muhalli hadin gwiwar Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, ACReSAL, da Bankin Duniya.

Ministan wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gudanarwar kwamitin ya bayyana jin dadinsa kan yadda hadin gwiwar za ta gyara ɓarnar da ke aukuwa a jihohin Arewa 19 ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Lawal ya ce akwai kasa hekta miliyan bakwai da aka lalata; don haka akwai buƙatar haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da ACRESAL don samar da damar gyara kasar daya gurɓace .

A cewarsa “Muna bukatar jaddada hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na Jihohi kuma ina fata wannan hadin gwiwa zai kai ga kananan hukumomi,” inji shi.

Tun da farko a jawabinsa Manajan Ayyuka na Bankin Duniya Mista Taimur Samad, ya ce aikin na ACReSAL wani shiri ne da zai kawo sauyi ,tare da farfado da kasar data gurbace.

Ya ce Bankin Duniya na ci gaba da kara kaimi kan sauyin yanayi, da cigaba da samar da daidaito da zai rage zafin sauyin na yanayi.

Samad ya bukaci jihohi 19 da babban birnin tarayya Abuja da su tabbatar da sun sabunta alkawurran aiwatar da ayyukan da ya shafi dumamarna yanayi.

A jawabinsa babban jami’in kula da ayyukan ACRESAL na kasa Mista Abdulhamid Umar, ya bayyana cewa aikin hadin gwiwar ma’aikatu uku wadanda ke gudanar da aikin wanda suka hada da ma’aikatun muhalli, albarkatun ruwa ,tsaftar muhalli noma da samar da abinci.

Ya ce ana kaddamar da aikin ne a jihohin arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Written by:

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Lets Chat
1
Need Help?
Help Center
Hello, welcome to SobiFm.How can we be of Help?